Wasu sojojin Najeriya sun nuna goyon baya ga zanga-zangar da za a yi saboda matsin rayuwa
Daga Sabiu Abdullahi
Wasu jami’an sojin Najeriya sun bayyana goyon bayansu ga zanga-zangar adawa da gwamnati da ake shirin yi a fadin kasar, bisa la’akari da irin kuncin rayuwa da rashin shugabanci da ake fama da shi a kasar.
Zanga-zangar mai taken “A Kawo Ƙarshen Rashin Iya Mulki a Najeriya” an shirya gudanar da shi ne daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta.
A cewar sojojin, wadanda suka nemi a sakaya sunansu, sun kuma nuna cewa suna cikin matsalar tabarbarewar tattalin arziki da rashin shugabanci.
Suna da’awar cewa gwamnatocin da ke kan mulki da na baya sun talautar da ma’aikatan soji masu karamin karfi, lamarin da ya tilasta musu sayar da kadarorinsu domin biyan bukatun yau da kullum.
Sojojin sun bayyana wani mummunan halin da ake ciki a barikin sojoji, inda da yawa ke ta faman biyan kudin karatun ‘ya’yansu da kayan masarufi.
“Akwai yunwa a duk barikin sojoji a yanzu haka, sojoji suna sayar da dukiyoyinsu domin su rayu har zuwa karshen watanni,” in ji wani soja.
Sojojin sun bayyana goyon bayansu ga zanga-zangar da za a yi, inda daya ya bayyana cewa, “Duk ‘yan Najeriya su sani akwai yunwa a bariki, mu mutane ne kamar kowane dan Najeriya, albashi da alawus-alawus dinmu ba su da yawa.
Wani kuma ya kara da cewa, “kusan kashi 97% na sojoji ne ke goyon bayan wannan zanga-zangar da za a yi ranar 1 ga watan Agusta saboda rashin albashi da alawus alawus.”
Sojojin sun bukaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da ‘yancinsu na yin zanga-zanga, suna masu cewa, “Wahalhalun da ake fama da su ya isa kuma ba za a amince da su ba.”