January 15, 2025

Wani mutumi ya ɗirka wa ɗiyarsa mai shekaru 17 ciki

0
Ganiyu-Aikore.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Wani lamari mai ban mamaki ya faru a unguwar Mokola Isale Tapa da ke garin Abeokuta a jihar Ogun, yayin da aka tsare Ganiyu Aikore bisa zarginsa da yi wa ɗiyarsa mai shekaru 17 ciki.

A cewar majiyoyi daga rundunar ‘yan sanda, Aikore a lokacin ya samu labarin cikin ‘yarsa ya nemi maganin zubar da ciki daga wani kantin magani da ke kusa da su.

Saboda fargabar yiwuwar zubewar cikin, ‘yar, tare da mazauna yankin da abin ya shafa, sun tuntubi shugabannin al’umma don kai rahoto game da lamarin.

Da yake daukar matakin gaggawa, wanda aka kai wa rahoton ya raka yarinyar zuwa sashen ‘yan sanda na Adatan domin shigar da kara a hukumance akan mahaifinta.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Omolola Odutola, ya tabbatar da kamun mahaifin nata.

Ya kuma bayyana cewa cikin da yake jikin yarinyar ya kai makonni 23.

“Mun kama shi, ana zarginsa da yin lalata da ‘yarsa na tsawon lokaci, kuma cikin ya kai makonni 23. Muna ci gaba da bincike,” in ji Odutola a ranar Laraba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *