December 7, 2025

Wani mummunan harin Isra’ila ya raunata ɗan jaridar Al Jazeera

image_editor_output_image501332307-1702664149535.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Rahotannin da ke fitowa daga Gabas ta Tsakiya ya nuna wani harin sama da ƙasar Isra’ila ta kai ya raunata ɗan jaridar Al Jazeera mai suna Wael al Dahdouh.

A cewar wani rahoton TRT Hausa, lamarin ya rutsa da shi ne yayin da yake daukar rahoto kan hare-haren Isra’ila a yankin Khan Younis na Gaza.

Rahoton na TRT ya ƙara da cewa, wani hari da Isra’ila ta kai kudancin Gaza ranar 25 ga watan Oktoba ma ya kashe masa matarsa da ɗansa da ƴarsa.