Wani Matashi Ya Ƙwaƙwale Idon Ƙanwarsa A Bauchi
Wani matashi mai suna Auwalu ya ƙwaƙwale idon ƙanwarsa mai suna Ruƙayya, yarinya ‘yar shekara bakwai, a garin Wailo, ƙaramar hukumar Ganjuwa, jihar Bauchi.
Da yake magana da manema labarai a Bauchi, Mahaifin yarinyar, Muhammad Adamu, ya bayyana cewa wanda ake zargi wa ne ga yarinyar, wato suna da uwa ɗaya uba ɗaya.
A cewarsa, Auwalu ya ja Ruƙayya ne zuwa cikin daji, inda ya ƙwaƙwale mata idanuwanta guda biyu.
Likitocin ido sun riga sun yi mata aiki.
Dr. Shahir Umar Bello, ƙwararren likitan ido kuma shugaban sashen kula da lafiyar ido na asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, ya tabbatar da cewa ganinta ba zai sake dawowa ba.
A cewarsa, hakan na nufin cewa Ruƙayya ta makance gaba ɗaya.




