February 16, 2025

Wani kamfanin sufurin jirgin sama ya haramta wa ƴan Nijeriya amfani da Ghana-masgo

188
IMG-20231203-WA0007.jpg

Muhammad Mahmud Aliyu

Kamfanin sufurin jiragen sama mallakar ƙasar Habasha, wato Ethiopian Airlines, ya haramta wa fasinjojinsa ‘yan Nigeria amfani da jakar Ghana-Masgo.

Sanarwar haramcin ta zo ne a wata takarda da Manajan harkokin filayen jirgi na kamfanin mai kula da shiyyar Legas Henok Gizachew ya tura wa manajan shiyya na Hukumar Filayen Jirage ta Nijeriya.

Kamfanin ya bayyana cewa, amfani da nau’in waɗannan jakunkuna yana jawo musu babbar asara, ta hanyar lalata na’urorin da suke ɗaukar kaya zuwa cikin jirgi ko fito da su daga jirgin.

Sanarwar ta ƙara da cewa, ba wai kamfaninsu kaɗai jakunkunan suke jawo wa asara a Nijeriya ba, har da wasu kamfanonin jiragen.

Sai dai kamfanin ya ce matafiya za su iya amfani da jakar matuƙar za su sanya ta a cikin kwali ko dai wani abu mai kusurwa huɗu wanda ba zai lalata musu kayan aiki ba.

A shekarar 2017 ne dai kamfanonin jiragen sama na KLM da Air France suka sanya irin wannan doka, bisa hujjar cewa jakunkunan za su iya yagewa, wanda hakan kuma zai iya jawo kayan ciki su riƙa faɗowa tare da haddasa matsala ga na’urorinsu na ɗaukar kaya.

188 thoughts on “Wani kamfanin sufurin jirgin sama ya haramta wa ƴan Nijeriya amfani da Ghana-masgo

  1. <a href=http://szotar.sztaki.hu/en/node/add/forum?gids=270123/>Легальная покупка диплома о среднем образовании в Москве и регионах

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *