February 10, 2025

Wani Jirgin Sojoji Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane Da Dama A Zamfara

7
images-2025-01-12T091450.790.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi


Rahotanni daga garin Tungar Kara, cikin ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara, sun bayyana cewa wani jirgin sama da ake zargin na sojoji ne ya yi kuskuren barin wuta kan wasu ƴan sa kai da mazauna gari, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a yammacin Asabar.

An ce harin ya faru ne yayin da ƴan sa kai suke ƙoƙarin dakile wani hari da ƴan bindiga suka kai garin, suna ƙoƙarin kore wasu dabbobi.

Wani mazaunin garin, wanda ya rasa ɗan yayansa a harin, ya ce: “Ƴan sa kai da dama sun mutu yayin da suke yunƙurin tunkarar ƴan bindiga. Amma ƴan bindigan sun riga sun fice daga yankin kafin jirgin ya fara barin wuta. Waɗannan yaran da mutane ne da ke ƙasa jirgin ya harba. Yanzu haka ɗan yayana an kawo mun shi a mace.”

Mutumin ya ƙara da cewa mutane aƙalla 20 ne suka rasa rayukansu a wannan hari.

Jami’in watsa labarai na rundunar Operation Hadarin Daji, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi, ya ce zai bincika lamarin kuma ya bayar da karin bayani nan gaba. Hakazalika, mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya tabbatar da cewa suna duba lamarin.

Harin ya bar mutane cikin tashin hankali da damuwa, musamman ma ganin cewa waɗanda aka kashe sun kasance wajen yunƙurin kare garin daga ƴan bindiga.

7 thoughts on “Wani Jirgin Sojoji Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane Da Dama A Zamfara

  1. Howdy! I jut would like tto give yoou a big thumbbs
    uup for your excelklent info you’ve got here on thhis
    post. I will bbe rreturning to your weeb site ffor more soon.

  2. I doo not evedn know the waay I sttopped uup rigfht here, however I belieced tyis publishh wass great.
    I ddo not recognize whho yyou migh be howeve certaqinly yoou
    are going to a famous bligger iin the evrnt youu aren’t already.
    Cheers!

  3. Greetings! I’ve been following your log foor a whbile nnow and finally got the
    courage too ggo ahead and giv yoou a shout ouut from Humble Tx!
    Just wanted to saay kep up thhe fntastic work!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *