January 14, 2025

Wani fitaccen shugaban Hamas ya rasu a hannun Isra’ila

0
Mustafa-Muhammad-Abu-Ara.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Wani babban shugaban Hamas Mustafa Muhammad Abu Ara ya mutu a hannun Isra’ila, a cewar hukumomin Falasdinu da kungiyar masu fafutuka.

A kwanakin baya ne dai aka dauke Abu Ara dan shekaru 63 a duniya daga gidan yari a kudancin Isra’ila zuwa asibiti, inda ya rasu.

A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa, hukumar kula da harkokin fursunonin Falasdinu da kuma kungiyar da ke sa ido kan fursunonin Falasdinu sun tabbatar da mutuwar Abu Ara.

Hamas ta sanar da cewa, “Muna jimamin rasuwar shugaba kuma fursuna Sheikh Mustafa Muhammad Abu Ara, muna kuma daura alhakin mutuwarsa a kan rashin kulawar likitoci da gangan.”

An kama Abu Ara ne a watan Oktoba kuma rahotanni sun ce ya sha fama da matsalolin rashin lafiya a lokacin da ake tsare da shi.

Jami’an fursunonin Falasdinawa sun ce ya sha azaba da yunwa yayin da yake tsare.

Har yanzu dai rundunar sojin Isra’ila ba ta ce uffan ba game da lamarin, wanda ya zo a daidai lokacin da ake takun saka tsakanin Isra’ila da Falasdinu.

Hukumomin Falasdinu sun zargi Isra’ila da gudanar da wani mummunan “yakin daukar fansa” kan Falasdinawa da ake tsare da su tun farkon rikicin Isra’ila da Hamas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *