November 8, 2025

Wani Da Ake Zargin Dan Damfara Ne Ya Mika Kansa Ga EFCC a Gombe

images (28)

Wani mutum mai suna Idris Adamu, wanda ake zargi da aikata damfara ta hanyar raba takardun bogi na ɗaukar aiki, ya mika kansa ga hukumar EFCC a jiya Litinin a shiyyar hukumar da ke Gombe.

Mai magana da yawun EFCC, Mista Dele Oyewale, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Abuja.

A cewar sanarwar, Idris Adamu ya isa harabar ofishin EFCC da misalin ƙarfe 1:00 na rana, inda ya nemi ganawa da Mukaddashin Daraktan Yanki, DCE Sa’ad Hanafi Sa’ad, domin bayyana wasu abubuwa da ya boye dangane da laifukan da ya aikata.

“Na zo ne domin tuba daga zunubaina kuma in bayyana gaskiya ga EFCC,” in ji Adamu yayin da yake bayyana kansa a gaban Daraktan Yanki.

Ya bayyana cewa ya karɓi kuɗi har naira miliyan tara daga mutane daban-daban, da nufin basu guraben aiki a hukumomin gwamnati, duk da cewa bai da wata madafa ta hakikanin guraben aikin.

Ya ce yana jin tsoron EFCC, lamarin da ya sa ya yanke shawarar bayyana gaskiya da mika kansa ga hukumar.

Mista Oyewale ya ce mukaddashin daraktan yankin ya nuna godiya ga wanda ake zargin saboda bayyana gaskiya, kuma ya bayar da umarnin a kai shi sashen bincike domin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

EFCC na ci gaba da jan hankalin jama’a su guji fadawa cikin ayyukan damfara tare da tabbatar da cewa doka za ta yi aiki ba tare da la’akari da matsayin wanda ake zargi ba.