Wani Asibiti A Najeriya Ya Yi Barazanar Binne Gawarwakin Da Har Yanzu Suke Macuware

Daga Sabiu Abdullahi
Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Kwara da ke Ilorin ya ba da wa’adin makonni biyu ga mutane su zo su karbi gawarwakin ‘yan uwansu.
A cewar rahoton, ɗakin ajiyar gawarwakin asibitin ya cika ƙwarai, babu sauran wuri saboda yawancin gawarwakin masu su ba su zo sun dauka ba.
Shugaban Sashen Hulɗa da Jama’a, Yakub Aliagan, ya bayyana cewa, “Hukumar Gudanarwar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Kwara, Ilorin, na sanar da jama’a cewa ɗakin ajiyar gawarwakinmu ya cika matuƙa, babu sauran wuri saboda gawarwakin da ba a karɓa ba.”
Asibitin ya roƙi jama’a su hanzarta zuwa su karbi gawarwakin ‘yan uwansu daga ranar Lahadi, 8 ga Disamba, zuwa ranar Asabar, 21 ga Disamba, 2024. Idan aka gaza yin haka, asibitin na iya ɗaukar matakin yi wa gawarwakin jana’iza ta gaba ɗaya.