March 28, 2025

Wani Abin Fashewa Ya Hallaka Dalibi A Abuja

FB_IMG_1736179528324.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Wani abin fashewa a wata makarantar Islamiyya da ke unguwar Kuchibiyu a Karamar Hukumar Bwari ta Abuja ya yi sanadin mutuwar dalibi daya tare da jikkata wasu hudu, in ji majiyoyin da suke da masaniya kan lamarin.

Fashewar ta faru ne da misalin karfe 12 na rana a ranar Litinin, 6 ga Janairu, 2025, a makarantar da ke kimanin kilomita 42 daga tsakiyar birnin Abuja.

Jami’an ceto, ciki har da tawagar kwararru kan abubuwan fashewa daga ‘yan sanda, sun garzaya wurin da lamarin ya faru, inda aka kai wadanda suka jikkata zuwa asibiti domin samun kulawa.

Duk da cewa hukumomi ba su fitar da wata sanarwa ba a kan abin da ya faru, wata majiya daga bangaren tsaro ta bayyana cewa, “Dalibin da ya rasa ransa, wanda ba a san sunansa ba tukuna, ya dauki wani abu da ake zargin abin fashewa ne, wanda ya fashe ya kuma jikkata sauran daliban, tare da haddasa firgici a makarantar.”

An kasa samun wani karin bayani daga hukumomin makarantar kan lamarin. Haka nan, kira da aka yi wa mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, Josephine Adeh, ya ci tura.

19 thoughts on “Wani Abin Fashewa Ya Hallaka Dalibi A Abuja

Comments are closed.