December 7, 2025

Wani Ɗan Najeriya Ya Kashe Mahaifinsa Tare Da Jikkata ‘Yan Uwansa A Amurka

40546

Rundunar ‘yan sanda ta New Orleans a Amurka ta kama wani matashi ɗan Najeriya mai suna Chukwuebuka Eweni, wanda ake zargi da kashe mahaifinsa tare da jikkata ‘yan uwansa mata biyu a gidansu da ke Pebble Street.

Iyalan sun shaida wa WWL Louisiana cewa mamacin, Samuel Eweni, malami ne na computer sciences a jami’ar Southern University a New Orleans. Sun tabbatar da cewa ‘ya’yansa mata biyu sun tsira daga harin.

Iyalan sun kuma ce duk da cewa matashin yana fama da matsalar tabin hankali, bai taɓa nuna tashin hankali ba.Rahotanni sun nuna cewa ɗaya daga cikin ‘yan uwansa an sallame ta daga asibiti, yayin da ɗayar ke ci gaba da jinya amma ana sa ran za ta warke.

Rundunar NOPD ta tabbatar da gano wanda ake zargin a Jefferson Parish.Jami’ai sun ce sun samu ƙiran gaggawa game da harin. Sun isa sun tarar da namiji baligi ba ya motsi saboda caccakar wuƙa, tare da mata biyu da suka samu rauni.

An garzaya da mata biyun asibiti domin ba su gaggawar kulawa.

Ofishin Coroner na Orleans Parish zai fitar da cikakken bayanin mamacin da musabbabin mutuwarsa bayan kammala binciken gawar.