Wani ɗan Boxing da ya sauya jinsi ya yi wa abokiyar hamayyarsa dukan-kawo-wuƙa
Katib AbdulHayyi
Wani dan kasar Aljeriya, mai suna Imane Khelifa da ya sauya jinsi zuwa mace, ya yi wa abokiyar karawarsa rugu-rugu a wani bidiyo da ya bayyana a shafin X.
Bidiyon ya biyo bayan sahale masa da hukumar boxing ta yi don ya halarci gasar Olympics ta wannan shekara a matsayin mace.
Tun farko dai hukumar gudanar da gasar ta haramtawa Khelif na Aljeriya da Lin Yu-Ting na Taiwan shiga gasar ta mata, sakamakon gwaji da ya nuna kwayoyin halittarsu na maza ne, duk da kuwa sun shelanta sauya jinsi daga maza zuwa mata, amma daga bisani aka ba su dama.
Sai dai jim kadan bayan sahalewar ne wani bidiyo da ya yi wadari a shafin X ya nuna yadda Khelifa yake surfer wata abokiyar damben boxing dinsa, Brianda Tamara, ‘yar kasar Italiya a shekarar 2022 ya jawo cece-ku-ce.


