January 24, 2025
IMG-20240520-WA0019.jpg


Daga Sulaiman Mahir

Ya zama shugaban rikon kwarya na kasar Iran a ranar 20/5/2024, bayan rasuwar shugaban kasar Ibrahim Ra’isi a wani hatsarin jirgin sama a ranar 19/5/2024.

Mohmmad Mokhber ne mataimakin shigaban kasa na farko. Kuma ya hau wannan mukami ne sakamakon nada shi da marigayi shugaba Ibrahim Raisi  ya yi a shekarar 2021, bayan ya yi nasarar lashe zabe.

Mokhber ya kasance na gaba-gaba wajen alaka kulla wa da kyautata alaka da hada-hadar makamai tsakanin Iran da Rasha.

An haifi Mokhber a shekarar 1955, yana da shekaru 68 yanzu.
Kamar Ra’isi, ana Kallon Mokhber a matsayin mai karfin alaka da shugaban Musulunci na Iran, Ali Khamna’i.

A shekarar 2010, Kungiyar tarayyar Turai ta EU ta sanya masa takunkumi bisa zargin sa da taka rawa a yunkurin Iran na mallakar makaman nukiliya, kafin daga bisani a dage su bayan shekaru biyu.

Kamar yadda kundin tsarin mulkin Iran ya tanada, shugaban rikon kwarya, Mokhber, da alkalin alkalai da shugaban majalisa za su shirya sabon zaben samar da wanda zai maye gurbin marigayi Ra’isi a cikin kwanaki 50.

Saboda dacewar ra’ayi da dadaddiyar alaka, ana sa ran Mokhber ya samu goyon bayan shugaban Addinin Iran, Ali Khamna’I, duk da yake wasu masharhanta na cewa komai zai iya faruwa.

Mokhber ya fito daga yankin Khuzestan, kwararren injiya ne, kuma yana da shaidar digirin digirgir har biyu a fannoni daban-daban.

A shekarun alif da dari tara, Mokhber ya yi aiki da sojojin juyin juya hali, kuma ya rike mukamin mataimakin gwamnan yankin Khuzestan. Haka kuma ya rike mukamin shugabn bankin Sina a shekarar 2000 na tsawon shekaru goma.

Masana ba sa ganin yiwuwar sauyuwar abubuwa daga yadda kasar Iran ke gudanadar manufofinta sakamakon rasuwar Ra’isi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *