November 8, 2025

Wajibi ne a kare martaba Sarkin Musulmi–Kashim Shettima

image_editor_output_image1063031518-1719237873429.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Mataimakin Shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya fada wa gwamnatin jihar Sokoto cewa ya zama dole a kare martabar Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III.

A cewar rahotanni, Shettima ya bayyana hakan ne a wani taron Zaman Lafiya da Tsaro na Arewa Maso Yammacin ƙasar, wanda ake yi a jihar Katsina a yau Litinin.

A cewarsa, “A duk wasu batutuwa na ci gaba a ƙasar nan, ina so na yi amfani da wannan damar don nuni da Mai Girma Sarkin Musulmi a matsayin misali, in kuma gode wa sarakunanmu da suka nan wajen.”

“Saƙona ga mataimakin gwamnan Sokoto mai sauƙi ne. Sarkin Musulmi ya fi gaban a kira shi Sarkin Sokoto kawai. Shi wata majinga ce da dukkanmu muke buƙatar kare martabarsa don ci gaban ƙasarmu.”

2 thoughts on “Wajibi ne a kare martaba Sarkin Musulmi–Kashim Shettima

  1. Diego Maradona y su famosa ‘Mano de Dios’ marcaron un hito en la historia del fútbol | La carrera de Diego Maradona inspiró a generaciones de futbolistas | Diego Maradona dejó su huella en el fútbol argentino y mundial | Diego Maradona es sinónimo de fútbol y pasión Diego Maradona mejor futbolista.

Comments are closed.