WAEC ta fidda sakamakon jarabawar bana
Daga Abdullahi I. Adam
Hukumar jarabawa ta ƙasashen yammacin Afirka, WAEC ta sanar ta fitar da sakamakon jarabawar bana ta ɗaliai na makarantun sakandire wadda aka gudanar a watannin Mayu da Yuni.
Kamar yadda hukumar ta wallafa a shafinta na X, hukumar ta sanar da cewa ɗalibai za su iya bincika sakamakon nasu daga yau Litinin.
Saƙon hukumar ya sanar da cewa “Hukumar jarabawa ta ƙasahen Yammacin Afirka tana sanar da ɗalibai waɗanda suka rubuta jarabawa ta shekarar 2024 cewa a yau Litini 12 ga Agusta 2024, an fitar da sakamakon jarabawar.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumar ba ta fitar da cikakkun alƙaluma na yawan ɗaliban da suka samu nasara ba kamar yadda ta saba.