Uwargidan Tinubu ta ba wa ɗalibai marasa galihu tallafi a Nasarawa
Uwargidan Shugaba kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta rarraba wa ɗalibai marasa galihu littafan rubutu a Jihar Nasarawa.
Remi Tinubu wadda ta bayyana samar da nagartaccen ilimi a matakin farko a matsayin tubalin ci gaban ƙasa.
Ta yi rabon littafan rubutun ne guda 60,000 ga ɗalibai marasa galihu a faɗin ƙananan hukumomi 13 na Jihar Nasawara.
Da take ƙaddamar da rabon littafan, uwargidan shugaban ƙasar, wadda matar Gwamnan jihar Nasarawa, ta wakilta, ta ce ilimi a matakin farko wani bigire ne da ke da muhimmanci wajen bunƙasar kasar nan.
Remi Tinubu ta jaddada ƙudirin Gwamnatin kasar nan, a dukkan matakai wajen bunƙasa harkokin ilimi ta fuskar inganci da kuma sauƙi musamman a tsakanin waɗanda ke da rauni a cikin al’umma.

