January 14, 2025

UWAR BARI: Majalisar Denmark ta saka hannu kan dokar hana wulaƙanta Al Ƙur’ani a bainar jama’a

0
images-2023-12-09T080504.190.jpeg

Daga Katib AbdulHayyi

Dokar da aka yi wa laƙabi da “Qur’an Law” an rattaɓa mata hannu ne bayan ƙona Al Ƙur’ani mai girma a bainar jama’a har sau 500 a cikin watanni biyar kacal da aka yi a ƙasar ta Turai.

Denmark na ɗaya daga ƙasashen da suka yi ƙaurin suna wajen nuna ƙiyayya ga Addinin Musulunci a gwamnatance da kuma wajen ɗaiɗaikun mutane.

Idan ba a manta ba a watan Satumbar shekarar 2010 an yi wani zanen ɓatanci ga Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wa Alihi Wasallama, inda ya jawo zanga-zanga daga duk ƙasashen Musulmi a faɗin duniya tare da kauracewa sayan kayayyakin ƙasar.

Shin za a iya cewa ƙasar Denmark ta sassauta ra’ayinta ne game nuna wa Addini ƙyama?

Abinda ya bayyana na dai shi ne, ƙasar ta sanya wa wannan doka ne don gudun kada wasu Musulmi su fusata su fara kai hare-haren ƙunar baƙin wake ko na harbe-harbe kamar yadda ya yi ta faruwa a ƙasar Faransa bayan ƙasar ta goyi bayan ɓatanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *