UEFA ta karrama Ronaldo saboda ya fi kowa zura kwallayea gasar
Daga Sabiu Abdullahi
Shahararren dan wasan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo, ya fito a dandalin sada zumunta a yau inda ya nuna godiya da karrama shi bayan samun lambar yabo daga gasar cin kofin zakarun Turai ta UEFA saboda kasancewarsa wanda ya fi kowa zura kwallaye a gasar.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Ronaldo ya rubuta cewa: “An girmama ni da samun wannan lambar yabo daga gasar zakarun Turai ta UEFA saboda kasancewarta wanda ya fi kowa zura kwallaye a gasar.”
Wannan nasarar ta sake nuna wani muhimmin ci gaba a hazakar da Ronaldo ya yi, inda ya karfafa matsayinsa na daya daga cikin manyan ‘yan wasan kwallon kafa a kowane lokaci.