Turkiyya za ta shiga shari’ar da Afirka ta Kudu ke yi kan Falasɗinawa
Daga Sodiqat Aisha Umar
Ƙasar Turkiyya za ta shiga shari’ar da Afirka ta Kudu ke yi da Isra’ila kan kisan kiyashi
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya sanar da matakin Turkiyya na haɗa kai da Afirka ta Kudu domin ci gaba da ƙalubalantar Isra’ila a gaban Kotun Duniya kan batun kisan kiyashin Isra’ilar.
Fidan ya bayyana cewa a lokacin tattaunawarsa ta diflomasiyya da ƙasashen da suka amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa, daga ciki har da Ƙungiyar Haɗin-kan Ƙasashen Musulmi ta OIC da ta Tarayyar Ƙasashen Larabawa, wasu daga cikin ƙasashen sun nuna shirinsu na ɗaukar matsaya dangane da batun
A yayin da yake sa ran samun ci gaba a shari’ar da ake yi a gaban Kotun Duniya, Fidan ya jaddada irin ƙoƙarin da Turkiyya ta jima tana yi domin shirya wa wannan matakin.