Tsohuwar ministar Buhari ta nesanta kanta daga zargin almundahanar naira biliyan 37
Daga Sabiu Abdullahi
Tsohuwar ministar harkokin jin kai, da ci gaban jama’a, Sadiya Umar-Farouq, ta musanta zargin cewa ta san wani dan kwangila da ake kira James Okwete, wanda ake zargi da almundahana.
Idan ba a manta ba, jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, sun kama Okwete bisa zargin karkatar da N37bn.
Umar-Farouk ta yi wannan martani ne a ranar Litinin a X, inda ta jaddada cewa ta yi wa al’ummar kasa hidima, inda ta ce a shirye take ta kare abin da ta aikata a duk lokacin da aka bukaci ta yi hakan.
“An samu rahotanni da dama da ke alakanta ni da wani bincike da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta yi a kan ayyukan wani James Okwete, wanda ba ni da masaniya a kai.
“James Okwete bai yi aiki ba, kuma bai wakilce ni ta kowace hanya ba.
“Ina alfahari da cewa na yi wa kasata hidima a matsayina na Ministar Tarayyar Najeriya da kowane irin alhaki kuma zan iya kare ayyukana da shirye-shiryena a lokacin da nake rike da mukamin a duk lokacin da aka kira ni da yin hakan.”




