January 15, 2025

Tsohon Shugaban NLC na Jihar Edo Ya Rasu Bayan Samun Taƙaddama da Ƴansanda

0
IMG-20240930-WA0022.jpg


Daga Sabiu Abdullahi
 
Kwamishinan Ƴansanda a Jihar Edo, Umoru P. Ozigi, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan mutuwar Kaduna Eboigbodin, tsohon shugaban Ƙungiyar Ƴan Ƙwadago (NLC) na jihar, bayan arangama da ya yi da ƴansanda a birnin Benin.
 
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa Eboigbodin ya rasu ne a lokacin da yake fuskantar ƴansandan, waɗanda ke neman takardun motarsa a wani bincike.
 
Majiyoyin sun ce Eboigbodin, wanda ke tare da matarsa a motar, ya nuna musu takardun motar, amma duk da haka sai da taƙaddama ta barke tsakaninsu.
 
Majiyoyin sun ce bayan haka, Eboigbodin ya fara jin haushi, kuma daga bisani sai ya fadi daga cikin motar.
 
Daga nan ƴansandan suka bar wurin, suka bar shi tare da matarsa, wadda ta garzaya da shi zuwa asibiti, inda aka sanar da ita cewa ya rasu.
 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *