Tsohon Shugaban Ƙasar Uruguay José Mujica (Pepe) Ya Rasu

Tsohon shugaban ƙasar Uruguay, José Mujica, wanda aka fi sani da “Pepe”, ya rasu yana da shekaru 89 a duniya.
José Mujica ya shugabanci ƙasar Uruguay daga shekarar 2010 zuwa 2015.
A zamanin mulkinsa, an fi saninsa da shugaba mafi ƙanƙan da kai a duniya, saboda yadda ya zaɓi rayuwa mai sauƙi da kauce wa amfani da dukiyar gwamnati.
Tuni dai aka jima da sanin cewa tsohon shugaban na fama da cutar daji, wadda a ƙarshe ta yi ajalinsa.
Mutuwar Mujica ta tayar da martani da jimami daga cikin gida da waje, duba da yadda ya shahara wajen kishin al’umma da adalci.