December 7, 2025

Tsohon Sanata Elisha Abbo ya zargi Kotun Ɗaukaka Ƙara da zama cibiyar “iya kuɗinka iya shagalinka”

images-109.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Elisha Abbo, sohon Sanata mai wakiltar Adamawa ta Arewa, ya zargi shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙara, Monica Dongban-Mensen da karbar cin hanci.

Rahotanni sun nuna cewa Abbo ya yi wannan zargin ne a ranar Laraba a wani taron manema labarai a Abuja.

Idan ba ku manta ba, kotun daukaka kara ta tsige shi ta kuma bayyana babban abokin hamayyarsa, Amos Yohanna, na jam’iyyar PDP a natsayin wanda ya ci zaɓen.

An tsige shi ne bayan an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben Sanata na shiyyar a watan Fabrairun 2023.

A cewar Abbo, kamar yadda rahotanni suka nuna, “kotun ta soke zabe a rumfunan zabe 253 ba tare da bayar da umarnin a sake gudanar da zabe ba, saboda sun san cewa na lashe wadannan mazabu ne, saboda sun san ko yau ko gobe ko jibi za a yi zabe, ni ne zan lashe zaɓen.”

Ya ce maishari’a Dongban-Mensen ta mayar da Kotun Daukaka Kara ta zama wata cibiyar kasuwanci, inda wanda ya fi ba da kuɗi shi ne zai samu nasara, ba wai don shi ne yake da gaskiya ba.