Tsohon ma’aikacin BBC Hausa ya rasu a Kaduna
Daga Abdullahi I. Adam
Kamar yadda kafar sadarwa ta BBC Hausa ta sanar yanzun nan, Allah Ya amshi ran Lawal Yusufu Saulawa wanda tsohon ma’aikacin tashar ne ta BBC.
Sanarwar ta bayyana cewa tsohon ma’aikacin ya rasu ne yau a gidansa da ke Badikko Kaduna.
Marigayin dai ya soma aiki ne da kafar ta BBC Hausa daga 1973 zuwa 1976. Haka nan kuma, marigayin ya taɓa riƙe muƙamin kwamishinan yaɗa labaran tsohuwar jihar Kaduna a 1980.
Cikin muƙaman da ya taɓa riƙewa akwai shugaban gidan rediyon Nagarta a jihar Kaduna da kuma muƙamai a hukumomin yaɗa labarai irin su VON da FRCN.
Marigayin ya rasu ya bar matan aure da ‘ya’ya da jikoki masu yawa.