Tsohon kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Ghali Umar Na’abba ya rasu
Daga Sabiu Abdullahi
Tsohon kakakin majalisar wakilai Rt. Hon. Ghali Umar Na’Abba, ya rasu.
Na’Abba, wanda shi ne shugaban majalisar wakilai ta biyu a jamhuriya ta 4 a yanzu.
A cewar majiyoyi, ɗan siyasar ya rasu ne a safiyar yau Laraba.
An zabe shi dan majalisar wakilai a shekarar 1999 daga jihar Kano.
Ya zama shugaban majalisar ne watanni kadan bayan kaddamar da majalisar bayan murabus din kakakin majalisar na wancan lokacin, Salisu Buhari daga jihar Kano, bisa badakalar satifiket na jabu.
Ya zuwa yanzu dai ba a iya samun cikakken bayanin rasuwarsa ba.