Tsohon gwamnan Kaduna Ramalan Yero ya koma jami’iyyar APC
Daga Abdullahi I. Adam
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Alh. Mukhtar Ramalan Yero ya bayyana cewa ya amince ya koma jam’iyyar APC.
Idan ba a manta ba, tsohon Gwamnan ya sanar da ficewa PDP ne a watannin baya duk da cewa ita ce jam’iyyar da ya riƙe manyan muƙamai ƙarƙashinta inda ya zamo kwamishina, mataimakin gwamna har zuwa matakin gwamna.
A faifan bidiyon da wani makusancinsa ya saki a kafar sadarwa ta Facebook, an jiyo tsohon gwamnan na faɗar cewa ya yanke wannan shawara e bayan ya tuntuɓi makusantansa a siyasance.