January 24, 2025

Tsohon gwamnan CBN Emefiele zai ci gaba da zama a gidan yari na Kuje saboda rashin biyan belin N300m

167
IMG-20231128-WA0011.jpg

Daga Ɗanlami Malanta

Kotu ta ɗage shari’ar tsohon shugaban bankin Najeriya zuwa ranakun 18 da 19 ga watan Janairun 2024 domin ci gaba da shari’ar saboda kasa biyan belin naira miliyan 300.

Emefiele yana fuskantar shari’a kan tuhume-tuhume shida da aka yi wa kwaskwarima kan zargin sayan motoci har na N1.6bn.

Sai dai ya musanta zargin da ake masa.

An bayar da belinsa ne a ranar 17 ga watan Nuwamba, 2023 kan naira miliyan 300 da kuma mutane biyu da za su tsaya masa, sannan a ci gaba da tsare shi a gidan yari na Kuje, har sai ya cika sharuddan belinsa.

A zaman da aka ci gaba da sauraren ƙarar, mai gabatar da ƙara, wanda babban jami’in hukumar kula da harkokin kasuwanci (CAC) ne, ya shaida wa kotun cewa Emefiele ba shi ne mai shi ko mai hannun jarin kamfanin na April1616 Investment Limited ba, wanda CBN ya ba shi kwangilar samar da motocin N1.2bn.

Lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo, ne ya jagorance shi a gaban shaidu yayin da yake gabatar da wasu takardu kan yadda aka kafa kamfanin a ranar 1 ga watan Agusta, 2016.

Ya kuma karanto sunayen masu hannun jarin kamfanin da suka haɗa da Aminu Yaro, Maryam Abdullahi, da Saadatu Yaro a matsayin masu hannun jarin kamfanin.

167 thoughts on “Tsohon gwamnan CBN Emefiele zai ci gaba da zama a gidan yari na Kuje saboda rashin biyan belin N300m

  1. можно ли купить диплом колледжа [url=https://4russkiy365-diplomy.ru/]можно ли купить диплом колледжа[/url] .

  2. купить диплом о среднем специальном образовании с занесением в реестр [url=https://4russkiy365-diplomy.ru/]купить диплом о среднем специальном образовании с занесением в реестр[/url] .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *