December 7, 2025

Tsadar rayuwa: An jibge ƴansanda sama da 4,000 a Abuja gabanin zanga-zangar da za a gudanar

Nigerian-police-750x414.webp

Daga Sabiu Abdullahi

Rundunar yan sandan Najeriya a birnin tarayya Abuja ta tura jami’anta har guda 4200 gabanin zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a farkon watan Agusta.

Rahotanni sun nuna cewa masu shirya zanga-zangar sun fada za a fara jerin gwano na tsawon kwanaki 10 daga ranar 1 ga watan Agusta.

A wata sanarwa ranar Juma’a, Josephine Adeh mai magana da yawun rundunar yan sandan birnin ta ce an jibge jami’an tsaron ne domin tsaron lafiyar jama’a, ta masu zanga-zanga da kuma hana bata gari shiga zanga-zangar.

Adeh ta ce Benneth Igweh kwamishinan yan sandan birnin ya tabbatarwa da mazauna birnin cewa jami’ansa za su kare rayuka da dukiya baza kuma su lamunci aikata barna ba.

Ta shawarci mazauna birnin da su kai rahoton duk wani motsi da basu yarda da shi ba.

Idan ba manta ba dai tun ainihi an shirya wannan gangami ne saboda tsananin tsadar rayuwa da ake fama da ita a Najeriya, kama daga tsadar man fetur har zuwa tsadar kayan masarufi.