December 7, 2025

Tsadar kaya ta tilasta wa masu yin burodi a Najeriya barazanar tsunduma yakin aiki

images-161.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Ƙungiyar masu gidajen burodi a Najeriya ta yi barazanar shiga yajin aikin gama-gari daga ranar 27 ga watan Fabarairu saboda lalacewar yanayin kasuwanci a ƙasar.

Chief Adeniyi Bamidele Gabriel, shugaban ƙungiyar ta ƙasa reshen jihar Kogi, ne ya bayyana haka ranar Talata.

Ya bayyana hakan ne a birnin Lokoja lokacin wani taron manema labarai.

Rahotanni sun nuna ya bayyana cewar ƙungiyar ta fara rufe shaguna saboda tsadar farashin kayan da “suke amfani da su wajen yin burodi kamar fulawa da sukari da yis da man ƙuli da man fetur da kuma dizel duk ta dalilin cire tallafin mai da kuma rashin daidaito a kasuwar canjin kuɗaɗde da yawan haraji ta hannun hukumomin gwamnati.”