June 14, 2025

Trump Zai Gana Da Putin A Saudiyya Kan Yakin Ukraine

trumpputin020825.jpg

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana shirin ganawa da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, a kasar Saudiyya domin tattauna hanyoyin kawo karshen yakin Ukraine.

Wannan mataki ya haifar da tambayoyi daga mutane da dama kan dalilin zabar Saudiyya a matsayin wurin tattaunawar.

Trump bai bayyana takamammen lokacin da za a gudanar da tattaunawar ba, sai dai ya ce yana iya yiwuwa a yi ta nan gaba kadan. Har ila yau, ya ce yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman, na iya kasancewa cikin taron.

Wannan bayani ya fito ne sa’o’i kadan bayan tattaunawar wayar da Trump ya yi da shugabannin Rasha da Ukraine, Vladimir Putin da Volodymyr Zelensky, a kokarin lalubo hanyar samar da zaman lafiya.

Saudiyya Ta Nuna Goyon Baya

A wata sanarwa da ta fitar, Saudiyya ta yabawa tattaunawar wayar da aka yi tsakanin Trump da Putin, tare da nuna goyon baya ga shirin gudanar da taron a kasar.

“Saudiyya na sake tabbatar da kudurinta na ganin an samu zaman lafiya mai dorewa tsakanin Rasha da Ukraine,” in ji sanarwar.

Dalilin Zabar Saudiyya

Rahotanni sun nuna cewa, baya ga Saudiyya, kasashe kamar China da Hadaddiyar Daular Larabawa sun nuna sha’awar karbar bakuncin tattaunawar tsakanin Trump da Putin.