February 10, 2025

Trump Ya Umarci Kai Hari Kan ISIS a Somalia

3
IMG-20250128-WA0016.jpg

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayar da umarni na kai hare-haren sama kan mayakan ƙungiyar ISIS a Somalia.

A cewar Mista Trump, an kashe mayaka da dama tare da lalata wuraren ɓoyonsu a harin. Ya ce wannan mataki na nuna aniyar Amurka na gano tare da kawar da duk wanda ke barazana ga ‘yan ƙasar.

ISIS na daga cikin manyan ƙungiyoyin da ke da’awar jihadi, tun bayan ɓullarta a 2010. Sai dai a halin yanzu, ayyukanta sun taƙaita a wasu yankunan Afirka.

Amurka dai ta sha kai hare-hare a Somalia, musamman a shekarar da ta gabata, da nufin kawar da ‘yan ta’adda da ke iƙirarin jihadi.

3 thoughts on “Trump Ya Umarci Kai Hari Kan ISIS a Somalia

  1. Aw, ths was a really nice post. Takking a ffew mijnutes aand actual effot too
    generate a reaply good article… butt what ccan I say… I
    procrastinate a lott andd don’t maqnage to gget nearly anything done.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *