Trump Ya Naɗa Susan Summerall Wiles a Matsayin Shugabar Ma’aikatan Fadar White House
Daga Sabiu Abdullahi
Zaɓaɓɓen shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da naɗin Susan Summerall Wiles a matsayin shugabar ma’aikatan fadar White House idan ya karɓi mulki a shekara mai zuwa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Trump ya bayyana Wiles da cewa “ta taimaka mani wajen lashe zaɓe tare da kafa sabon tarihi a siyasar Amurka. Mace ce mai ilimi da ƙwazon aiki, wadda ake girmamawa a duk duniya.”
“Ina da yaƙinin cewa za ta taimaka mani wajen dawo da martabar Amurka da kuma zama abin koyi,” in ji Trump.
Yanzu haka, kwamitin karɓar mulki na Donald Trump na ci gaba da aiki don zaɓo mutanen da za a naɗa a manyan mukamai a cikin sassa 15 na gwamnati, ciki har da Sakataren Harkokin Waje da kuma na Tsaro.