March 28, 2025

Trump Ya Ƙara Matsin Lamba Kan Shirin Iko da Gaza

image_editor_output_image141337383-1739180156968.jpg

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ƙara matsa lamba kan shirin da ke da nufin kwace iko da Zirin Gaza da kuma fitar da Falasɗinawa daga yankin, duk da suka da yake sha daga sassa daban-daban na duniya.

Trump ya bayyana wa manema labarai cewa yana da burin saye da mallakar Gaza domin hana Hamas sake samun tasiri a yankin.

Haka nan, ya jaddada cewa zai tabbatar da jin daɗin rayuwar Falasɗinawa tare da samar musu da zaman lafiya.

Bugu da ƙari, Trump ya bukaci ƙasashen Larabawa da su taka rawa a sake gina wani ɓangare na Gaza.

2 thoughts on “Trump Ya Ƙara Matsin Lamba Kan Shirin Iko da Gaza

Comments are closed.