January 15, 2025

Tinubu zai tafi Senegal don halartar bikin rantsar da shugaba mai jiran gado Faye

4
Tinubu-travels.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Shugaba Bola Tinubu zai bar Abuja ranar Talata 2 ga Afrilu, 2024, zuwa Dakar, Senegal, domin halartar bikin rantsar da zababben shugaban kasar Senegal, Bassirou Faye.

Fadar shugaban kasar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai baiwa Tinubu shawara kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya fitar mai taken ‘Shugaba Tinubu zai halarci bikin rantsar da zababben shugaban kasar Senegal Bassirou Faye.

Tinubu, wanda shi ne Shugaban Hukumar ECOWAS, ya ziyarci kasar a karon farko tun hawansa mulki, bisa gayyatar da gwamnatin Senegal ta yi masa.

“Zai bi sahun sauran shugabannin yankin don shaida bikin rantsarwa a Cibiyar Nunin Diamniadio ranar Talata,” in ji Ngelale. 

Shugaban kasar zai samu rakiyar ministan harkokin wajen kasar Yusuf Tuggar da wasu manyan jami’an gwamnati.

4 thoughts on “Tinubu zai tafi Senegal don halartar bikin rantsar da shugaba mai jiran gado Faye

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *