January 14, 2025

‘Tinubu yakan fita cikin dare don gane wa idonsa halin da talakawa ke ciki’—cewar Sanata Orji Kalu

1
ei_1729222621305-removebg-preview.png


Daga Sabiu Abdullahi

Sanata Orji Kalu ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu yakan fita da daddare don ganin halin da ‘yan Najeriya ke ciki da kansa.

Kalu, wanda ke wakiltar Mazabar Abia ta Arewa a Majalisar Dattawa, ya yi wannan jawabin ne a shirin Politics Thursday na Channels Television.

“Shugaban kasa da kansa ya san cewa ‘yan Najeriya na cikin wahala kuma suna fama da yunwa. Shi mutum ne mai sanin halin talakawa; yana da masaniya sosai game da abin da ke faruwa a titunan kasar,” inji Kalu. “Wasu lokutan shugaban kasa yakan shiga motarsa da daddare don zagayawa a Abuja domin sanin abin da ke faruwa.”

Wannan na zuwa ne bayan da Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya amince da cewa wasu manufofin gwamnati sun jefa ‘yan Najeriya cikin wahala, amma sun zama dole.

“Wasu daga cikin manufofin da aka dauka suna da zafi, amma kusan babu makawa sai an yi su,” inji Shettima. “Zuciyata da zuciyar Shugaba Bola Tinubu na tare da talakawan Najeriya. Muna jin irin halin da matasa da talakawa ke ciki.”

1 thought on “‘Tinubu yakan fita cikin dare don gane wa idonsa halin da talakawa ke ciki’—cewar Sanata Orji Kalu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *