January 15, 2025

Tinubu ya yi tir da yunƙurin hallaka Trump

0
GSdM-luWgAAzmqq.jpg_large.jpg

Daga Sodiqat Aisha Umar

Shugaban Bola Tinubu ya yi allawadai da yunƙurin kisan tsohon shugaban Amurka, Donald Trump.

Trump wanda ke yin takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar Republican, ya tsallake rijiya da baya bayan an harbe shi, yana cikin jawabi a wajen yaƙin neman zaɓe, a Pennsylvania, lamarin da shugaban Najeriyan ya bayyana a matsayin babban tashin hankali.

Tinubu ya bi sahun sauran shugabannin duniya wajen bayyana takaici a kan harin, yana mai cewa irin wannan rikici bashi da mazauni a turbar dimokuraɗiyya.

“Harin da aka kai wa tsohon shugaban Amurka, Donald Trump babban abin tashin hankali ne kuma ya saɓawa turbar dimokuraɗiyya.” inji Tinubu a saƙon da ya wallafa a shafin X.

Ya ƙara da cewa “Ina miƙa jaje na ga tsohon shuagaban ƙasar, kuma ina mashi fatan waraka cikin sauri. Ina kuma ta’aziyayya ga ƴan uwan wanda ya mutu da kuma fatan waraka ga waɗanda suka samu rauni.”

Shugaban ƙasan ya ce Najeriya tana tare da Amurka a wannan yanayi na alhini.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *