January 14, 2025

Tinubu ya tura wa Majalisa sunayen waɗanda za su jagoranci Hukumar Raya Arewa maso Yammacin Najeriya

0
FB_IMG_1720723074529-jpg

Daga Sodiqat A’isha Umar

Shugaban Bola Tinubu ya aike da sunayen shugabannin majalisar gudanarwar sabuwar hukumar raya yankin arewa maso yammacin Najeriya, zuwa ga majalisar dattawan domin amincewa da naɗinsu.

Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar ya ce matakin na zuwa ne bayan sanya hannu kan dokar da ta amince da ƙirƙiro sabuwar hukumar.

A ranar 24 ga watan Yuli ne dai Shugaba Tinubu ya sanya hannu kan sabuwar dokar.

Mutanen da Shugaba Tinubun ya aike da sunayensu don jagorantar sabuwar hukumar sun haɗa daAmbassada Haruna Ginsau ( daga nan jihar Jigawa) a matsayin shugaban majalisar gudanarwar hukumar.

Farfesa Abdullahi Shehu Ma’aji (daga jihar Kano) a matsayin shugaban hukumar.Da dai Sauran mambobin hukumar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa ana sa ran sabbin shugabannin za su yi amfani da ƙwarewarsu wajen gina sabuwar hukumar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *