Tinubu ya rantsar da Kekere-Ekun a matsayin sabuwar Alƙaliyar Alƙalai
Daga Sabiu Abdullahi
A yau ne Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu ya rantsar da Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun a matsayin sabuwar Alƙaliyar Alƙalan ƙasar ta riƙo, kafin Majalisar Dattawan ƙasar ta tabbatar da naɗin nata.
An naɗa ta a kan muƙamin ne bayan Alƙalin Alƙalan ƙasar Olukayode Ariwoola ya yi ritaya a jiya Alhamis.
Wace ce Kudirat?
An haifi Kudirat Motonmori Olatokunbo (CFR) a ranar 7 ga watan Mayun 1958 a birnin London da ke ƙasar Birtaniya.
Sannan an fi saninta da Kudirat Kekere-Ekun.
Ƙwararriyar lauya ce a Najeriya kuma mai shari’a ta Kotun Koli ta Najeriya.
A shekarar 1980, ta kammala digirinta na farko a fannin shari’a daga Jami’ar Legas, kuma ta samu gurbin karatu a Nigerian Bar a ranar 10 ga Yuli 1981, bayan ta kammala makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya.
Daga bisani ta wuce Makarantar Tattalin Arziki ta London inda ta samu digiri na biyu a fannin shari’a a watan Nuwamba 1983.