January 24, 2025

Tinubu ya nuna ‘alhini’ kan ambaliyar ruwa da aka yi a Maiduguri

0
FB_IMG_1720723074529

Daga Sabiu Abdullahi  

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana matukar damuwarsa kan yadda ambaliyar ruwa ta afku a wasu sassan Maiduguri, babban birnin jihar Borno a baya-bayan nan, ya kuma bayar da umarnin daukar matakin gaggawa domin shawo kan lamarin.  

A cikin wata sanarwa da mai ba wa Tinubu shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, ya ce shugaban kasar ya mika ta’aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar Borno musamman wadanda suka rasa rayukansu sakamakon bala’in.  

Shugaban ya yi kira da a gaggauta kwashe mazauna yankunan da lamarin ya shafa yayin da hukumomi ke ci gaba da tantance irin barnar da aka yi.

Ya kuma tabbatar wa Gwamna Babagana Zulum cewa gwamnatin tarayya a shirye take ta bada hadin kai wajen magance matsalolin jin kai ga wadanda ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu.  

Tinubu ya kuma umurci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) da ta kai agajin gaggawa ga wadanda abin ya shafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *