January 24, 2025

Tinubu ya naɗa Jim Ovia a matsayin shugaban asusun ba wa ɗalibai bashin karatu

0
20240424_151253.jpg

Daga Sodiqat Aisha Umar

Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗin Jim Ovia, CFR a matsayin shugaban asusun bai wa ɗalibai bashin karatu.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Kasa, Ajuri Ngelale, ya fitar, shugaba Tinubu ya ce yana da yaƙinin mista Ovia zai yi amfani da ƙwarewarsa ta aiki wajen ganin ɗaliban ƙasar sun samu damar faɗaɗa karatu ta hanyar samun bashi daga shirin da gwamnatinsa ta ɓullo da shi.

Mista Ovia – wanda fitaccen ma’aikacin banki ne, kuma ɗan kasuwa – yana da digiri na biyu a fannin kasuwanci daga kwalejin kasuwanci ta Harvard da ke Amurka.

Bai wa ɗalibai bashin karatu wani shiri ne da gwamnatin ƙasar nan ta ɓullo da shi, don bai wa ɗalibai damar yin karatu a manyan makarantun ƙasar nan, tare da samun cikakkiyar ƙwarewa, musamman tsakanin matasan ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *