January 15, 2025

Tinubu ya yi ‘murnar’ samun ƴancin ƙananan hukumomi

284
IMG-20240707-WA0010.jpg

Daga Sodiqat Aisha Umar

Shugaban Bola Ahmed Tinubu ya yaba da hukuncin Kotun ƙoli da ta tabbatar da ƴancin ƙananan hukumomi.

A sanarwar da fadar shugaban ta fitar bayan hukuncin a ranar Alhamis, shugaban ya ce hukuncin tamkar jaddada matsayin ƙaramar hukuma ne a kundin tsarin mulki.

A hukuncinta na ranar Alhamis, Kotun Ƙolin Najeriya ta ce iko da kuɗaɗen ƙananan hukumomi da gwamnoni ke yi ya saɓa wa kundin tsarin mulki.

Alƙalin da ya jagoranci hukuncin Emmanuel Agim ya ce ƙananan hukumomi 774 na Najeriya su ke da haƙƙin tafiyar da kuɗaɗensu da suke samu daga kason tarayya.

Shugaba Tinubu ya ce wannan mataki ne da ya tabbatar da matsayin ƙaramar hukuma a matsayin ɓangare na gwamnati da kuma tabbatar da shugabanci nagari.

Ya ce rashin sakin mara ga ƙananan hukumomi babbar matsala ce ga ci gaban ƙasa musamman yadda ba a jin tasirin gwamnati a karkara.

284 thoughts on “Tinubu ya yi ‘murnar’ samun ƴancin ƙananan hukumomi

  1. <a href=http://szotar.sztaki.hu/en/node/add/forum?gids=270123/>Легальная покупка диплома о среднем образовании в Москве и регионах

  2. диплом о высшем образовании с занесением в реестр [url=https://4russkiy365-diplomy.ru/]диплом о высшем образовании с занесением в реестр[/url] .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *