Tinubu ya isa Saudiyya don halartar taron tattalin arziki na duniya

Daga Sabiu Abdullahi
Shugaba Bola Tinubu ya isa Riyadh, babban birnin Saudiyya, a ranar Juma’a don halartar taron tattalin arzikin duniya na musamman na 2024 kan hadin gwiwar duniya, da bunkasa, da makamashi don ci gaba.
Wannan na zuwa ne yayin rangadin kasashe biyu bayan da ya kai ziyara a Hague, Netherlands, tun ranar Laraba.
Sama da shugabanni 1,000 daga kasuwanci, gwamnati, da fannin ilimi daga kasashe sama da 90 ne ake sa ran za su halarci babban taron da a Riyadh, wanda aka shirya yi a ranar Asabar da Lahadi.
Tattaunawar za ta ta’allaka ne kan ayyukan da aka yi tun lokacin taron farko na ci gaban da aka gudanar a Geneva, Switzerland, a cikin 2023.