January 15, 2025

Tinubu ya dawo Najeriya yayin da mutane ke cikin ƙuncin rayuwa da tsadar abinci

0
WhatsApp-Image-2024-02-06-at-21.46.50.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

A daren ranar Talata ne shugaba Bola Tinubu ya dawo Najeriya bayan wata ziyarar sirri da ya yi a birnin Paris na kasar Faransa na tsawon makonni biyu.

Jirgin shugaban kasar mai lamba NAF 001 ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin karfe tara na dare.

Shugaban ya samu tarba daga manyan jami’an gwamnati da suka hada da shugaban ma’aikatan fadar sa, Femi Gbajabiamila; Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume; Mai ba da shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike.

Duk da cewa fadar shugaban kasar ta yi shiru kan dalilin ziyarar, da ma an sa ran shugaban na Najeriya zai dawo “a cikin makon farko na watan Fabrairun 2024.”

Tafiyar dai ita ce ta uku da Tinubu ya kai kasar Faransa, kuma ziyararsa ta 14 a kasashen waje tun bayan hawansa mulki watanni takwas da suka gabata.

Ya dawo ne a yayin zanga-zangar da ake yi a wasu jihohin saboda tsadar abinci da tsadar rayuwa.

Bayan wani taro na ranar Talata, wanda shi ne na farko cikin jerin uku, Ministan Labaru Mohammed Idris ya shaida wa manema labarai cewa, “Kwamitin shugaban kasa ne na musamman don magance matsalar karancin abinci ko rashin isasshen abinci a gidajen mafi yawan ‘yan Najeriya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *