February 16, 2025

Tinubu ya ba da umarnin sakin yaran da aka kama a zanga-zangar #EndBadGovernance bayan ce-ce-ku-ce

7
IMG-20241102-WA0012.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ba da umarnin sakin gaggawa ga dukkan yaran da aka kama yayin zanga-zangar #EndBadGovernance a watan Agusta.

Ministan Labaru da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, ne ya sanar da hakan yayin wani taron gaggawa da aka gudanar a fadar Aso Rock Villa, Abuja.

Idris ya ce, “Shugaban kasa ya bada umarnin sakin dukkan matasan ba tare da la’akari da duk wani tsarin doka da ake bi ba.”

Tinubu ya kuma umarci Ma’aikatar Harkokin Jin Kai ta kula da walwalar matasan tare da tabbatar da haduwarsu da iyayensu ko masu kula da su.

Kwamitin gudanarwa zai binciki kamawa, tsarewa, da yadda aka yi mu’amala da yaran, kuma za a dauki matakin ladabtarwa kan duk wani jami’i da aka samu da laifi.

Umarnin ya zo ne bayan shari’ar wasu mutum 76, ciki har da yara 30 masu shekaru tsakanin 14 zuwa 17, da aka gurfanar bisa zarginsu da cin amanar kasa, lalata dukiyoyi, da tada hankali.

7 thoughts on “Tinubu ya ba da umarnin sakin yaran da aka kama a zanga-zangar #EndBadGovernance bayan ce-ce-ku-ce

  1. I wass extrekely pleased to discoover tthis site. I wahted
    to thamk yoou forr ones tme ffor this particularly fantatic read!!
    I defijitely really liuked eery llittle bitt oof it andd I have
    yoou book-marked to look aat new thinhgs iin you blog.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *