November 9, 2024

Thomas Tuchel zai raba gari da Bayern; Mbappe zai tafi Madrid

0

Rahotanni da ke fitowa daga Jamus na nuna cewa Thomas Tuchel zai bar Bayern Munich a karshen kakar wasa ta bana.

A cewar ɗan jarida Fabrizio Romano, bayan tattaunawa da matsaloli a cikin ‘yan kwanakin nan, FC Bayern da manajan sun yanke shawarar raba gari a watan Yuni.

“Mun amince cewa za mu kawo karshen zamanmu bayan karshen kakar wasa ta bana. Har zuwa lokacin, ni da ma’aikatana ba shakka za mu ci gaba da yin duk abin da za mu iya don tabbatar da mafi girman nasara,” a cewar Thomas Tuchel.

Hakan na nufin Bayern za ta nemi sabon koci ke nan.

A ɗaya ɓangaren kuma, Kylian Mbappé, a halin yanzu yana kammala shirye-shiryensa na komawa Real Madrid

Mbappé yana da yarjejeniyar kwantiragin Real Madrid a hannunsa tun daga watan Janairu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *