November 8, 2025

Tawagar Wasanni Ta Kano Ta Yi Hadari Inda Mutum 19 Suka Mutu

sr file - 2025-05-31T143707.174

Daga Sabiu Abdullahi

Akalla mutane 19 daga cikin tawagar wasanni ta jihar Kano sun rasa rayukansu a wani hadarin mota da ya afku a safiyar Asabar, 31 ga Mayu, 2025, a yankin karamar hukumar Kura, jihar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa hadarin ya faru ne lokacin da wata motar bas ɗin da ke ɗauke da ‘yan wasa da jami’ai ta fado daga gada.

Motar ita ce ta ƙarshe daga cikin motoci takwas da suka taso daga gasar wasanni da aka gudanar a jihar Ogun.

“Mun taso da dare daga jihar Ogun bayan kammala gasar wasanni ta kasa lokacin da hadarin ya faru,” in ji ɗaya daga cikin wadanda suka tsira, Ado Salisu.

“Kano ta zo da motoci takwas, kuma motar da ta yi hadarin ita ce ta ƙarshe.”

Shaidu sun tabbatar da cewa wadanda suka mutu sun haɗa da ‘yan wasa, ma’aikatan lafiya, ‘yan jarida da masu kula da harkokin wasanni.

Wasu da dama sun jikkata kuma aka garzaya da su asibitin Kura kafin daga bisani a mayar da su Asibitin Murtala don samun kulawa ta musamman.

Tawagar ta halarci gasar wasannin “Gateway Games” da aka shirya domin ƙarfafa haɗin kai da zumunci tsakanin jihohi a Najeriya.