Tausayi Ne Ya Sa Shugaba Tinubu Bada Umurnin Sakin Yara Kanana Da Aka Tsare–Kashim Shettima

Daga Sabiu Abdullahi
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa umarnin da Shugaba Bola Tinubu ya bayar na sakin yaran kanana da ake zargi da laifin cin amanar ƙasa ya samo asali ne daga tausayinsa.
Shettima ya yi wannan bayani ne a ranar Talata yayin da yake tarbar yaran a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ya soke tuhumar da ake musu.
Ya kuma yi bayanin cewa akwai bidiyo da hotuna da suka nuna ayyukan wasu daga cikin waɗanda suka yi zanga-zanga, waɗanda suka sanya wa kansu a yanar gizo.
Shettima ya bayyana damuwarsa game da yadda lalata kayan gwamnati da tsaida harkokin tattalin arziki da masu zanga-zangar suka yi ya janyo asarar fiye da naira biliyan N300 ga ƙasar.
Ya ce, “Shugaban ƙasa kuma Babban Kwamandan Askarawan Tarayyar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bada umarnin sakin waɗanda ake zargi bisa dalilai na jin ƙai, duk da kasancewar akwai bidiyo da hotuna waɗanda ba za a iya musantawa ba na ayyukan wasu daga cikinsu da suka dora a intanet.”
elektrik süpürgesi arıza Ümraniye Bakım sonrasında süpürgemin performansı arttı. https://melaninbook.com/read-blog/43977