April 18, 2025

Tashe-tashen hankula ya janyo hasarar rayuka sama 14 a Bokkos da ke Jihar Filato

images-2023-12-25T061432.362.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Aƙalla mutane 16 ne aka ruwaito sun rasa rayukansu a wani hari da aka kai cikin dare a kauyen Mushu da ke karamar hukumar Bokkos a jihar Filato.

An kai harin ne a lokacin da mazauna garin ke barci, lamarin da ya jefa al’ummar cikin halin kaka-nika-yi da alhini.

Kakakin rundunar ‘Operation Safe Haven’, Captain Oya James, ya tabbatar da faruwar wannan mummunan lamari, inda ya kara da cewa jami’an tsaro sun dauki matakin gaggawa domin hana afkuwar rikici a yankin.

Duk da tashe-tashen hankula da aka fara yi, yanzu an ce an shawo kan lamarin.

A halin da ake ciki, Gwamna Caleb Mutfwang ya yi Allah-wadai da harin, inda ya siffanta harin a matsayin zalunci.

A cikin wata sanarwa a hukumance ta hannun Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na gwamnan Gyang Bere, Gwamna Mutfwang ya nuna matukar damuwa tare da umurtar hukumomin tsaro da su gaggauta cafke wadanda suka aikata laifin.

Gwamnan ya jaddada bukatar maharan su fuskanci cikakken fushin doka tare da yin kira ga al’ummar jihar da su sa ido sosai.