‘Tallafin mai zai iya lamushe naira tiriliyan 5 a 2024’
Daga Sodiqat Aisha Umar
Ana sa ran tallafin man fetur zai lakume kimanin Naira tiriliyan 5.4 a shekarar 2024, a cewar Gwamnatin Tarayya.
Wannan ya saba wa Naira tiriliyan 3.6 da aka ware wa tallafin man a kasafin kudin shekarar 2023.
Wani daftarin rahoton shirin inganta ayyuka sufuri da sadarwa (ASAP) wanda Ministan Kuɗi, Wale Edun, ya gabatar wa Shugaba Tinubu a ranar Talata, ya nuna an biya kudaden tallafin mai na Naira tiriliyan 5.4 a shekarar 2024 Naira tiriliyan 5.4, wanda ya haura na 2023 da Naira tiriliyan 1.8.
An tsara shirin ASAP ne don magance manyan kalubalen da suka shafi yunkurin yin gyare-gyare da habaka cigaba a sassa daban-daban na tattalin arziki.
A cewar daftarin shirin ASAP da Edun ta gabatar ya haura ₦3.6 tiriliyan da aka kashe a 2023 da kuma ₦2.0 tiriliyan da aka biya a 2022.
A baya dai, Gwamnatin Tinubu ta tsaya tsayin daka cewa ba za ta kara ba da tallafin man fetur ba.
A watan Disamba, gwamnatin ta ce sabanin ikirarin da Bankin Duniya ya yi na cewa ta ci gaba da biyan tallafin.