January 14, 2025

TA LEƘO TA KOMA: Kotun ɗaukaka ƙara ta soke zaɓen gwamnan Jihar Filato

0
images-2023-11-19T160209.571.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi


Kotun daukaka kara da ke Abuja ta soke zaben gwamna Caleb Muftwang na jihar Filato a ranar Lahadi.

Kwamitin kotun mai mutane 3, ya yanke hukuncin cewa, Muftwang bai samu daukan nauyi da ya dace da doka ba daga jam’iyyar PDP, saboda sabawa sashe na 285(2) na kundin tsarin mulkin Najeriya.


Kotun ta bayyana cewa Nentawe Goshwe na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya yi nasarar daukaka karar da ya shigar, inda ya ce batun cancantar duk wani lamari ne da ya shafi gaba da kuma bayan zabe a karkashin sashe na 177 (c) na kundin tsarin mulkin Najeriya, 1999, da sashe 80 da 82 na Dokar Zabe, 2022.


Kwamitin ya amince da ƙarar wanda ya shigar da kara, Goshwe, inda ya nuna rashin bin umarnin babbar kotun jihar Filato da kuma kotun daukaka kara da PDP ta yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *